Dr. YAKUBU ALIYU GOBIR

A Doctor of African Cultures (Hausa)

Sunday, January 13, 2019

Da Abinmu Aka Gan Mu...: Darussan Haɗin Kai Daga Al’adun Hausawa

January 13, 2019 0 Historians as well as anthropologist affirm that the Hausas were living a life of mutual co-existence and assisting of one another. They help one another on matters concerning ceremonies, i.e. marriage and birth ceremonies, as well as condolence i.e. for death and/or any situation of depression. However, the cooperative practices amongst the Hausas include; eating together, teamwork and settling scores between individuals among host of others. An interesting phenomenon lies on the way younger ones are brought up with the orientation of mutuality. The younger ones eat, play as well as listen to folklores together. More so, any adult corrects whichever wrong they might do during these affairs. This had made the orientation of younger ones an easy task for the Hausas belief that, ‘the child….

Najasa A Mahad’in Maganin Iska

January 13, 2019 0Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu a kullum ƙara bunƙasa yake yi.  Lamarin iskoki abu ne da ya mamaye al’adun Bahaushe a rayuwarsa. Bahaushe na ganin iskoki wasu halittu ne masu ƙima da daraja ta musamman, da jin cewa suna iya cuta masa a rayuwa. A tunaninsa, cutukan da iskoki ke haddasawa su ne manyan cutuka, domin suna naƙasa rayuwa kuma suna da wuyar magani. Duk da samun wayewar kai da bunƙasar kimiyyar zamani, Bahaushe bai yarda akwai maganin iskoki a asibitocin nasara ba, ya fi son ya tunkari matsalar a Bahaushiyar al’ada. Najasa na ɗaya daga cikin hanyoyin al’ada da Bahaushe ke bi wajen warkar da cutar iskoki. Nazarin yadda Bahaushe ke amfani da najasa wajen sarrafa maganin iska shi ne maƙasudin wannan muƙalar.

Friday, January 11, 2019

Namijin Dare: Hulɗar Soyayya Tsakanin Ɗan Adam Da Iska

January 11, 2019 0Al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki. Tarihi ya nuna wannan hulɗa ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu karɓuwa sosai ga masana al’adun Hausawa. A yau, goshin ƙarni na ashirin da ɗaya Hausawa sun buɗe wani sabon shafi na hulɗa da iskoki. A da, ’yan bori da bokaye da malaman tsibbu su ke cin karensu ba babbaka a kan sha’anin hulɗa da iskoki. Yanzu an sami rukunin wasu malaman addini da suke hulɗa da iskoki ta hanyar ruƙiyya[1], domin warkar da cututtukan da…

Monday, December 31, 2018

Tubalan Iskoki a Ginin Littafin Ruwan Bagaja

December 31, 2018 0


Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu kullum sai ƙara bunƙasa yake yi saboda irin ƙoƙarin da masana da ɗaliban Hausa ke yi na rayar da su. Adabi kuwa, rumbu ne da ake hango rayuwar kowace irin al’umma da iri-iren abubuwan da take cuɗanya da su a rayuwarta. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin gaske, tamkar harshe ne da haƙori. Masana sun tabbatar da cewa al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki, kuma hulɗar, ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Maƙasudin wannan muƙala shi ne hango wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato yadda iskoki suka mamaye tunanin Bahaushe, har aka wayi gari, da wuya ya faɗi, ko ya rubuta, wata fasaha ko hikima, ba tare da ya saka iskoki a ciki ba. Hasali ma, saka iskokin shi ke haskaka fasahar da ya rubuta, kamar yadda littafin Ruwan Bagaja zai tabbatar.

Sunday, December 30, 2018

Al’adar Roƙon Ruwa A Ƙasar Gobir: Daga Riwayar Bakandamiyar Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba

December 30, 2018 0

Ƙasar Gobir wani yanki ne daga cikin garuruwan Hausawa na asali. Garuruwan Hausawa na asali nan ake samun Hausawa na asali waɗanda yanayin rayuwarsu da al’adunsu suka yi daidai da yadda Hausawa ke gudanar da su. Al’adar roƙon ruwa tana daga cikin al’adun da suka maƙale wa rayuwar Hausawa har bayan da Musulunci ya yi tasiri ga rayuwar tasu. Maƙasudin wannan takarda shi ne fito da yadda Gobirawa ke gudanar da wannan al’adar, ta bakin Malam Muhammad Umar Kwren-Gamba, daga Bakandamiyarsa.

Adabin RuƘiyya A Goshin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya

December 30, 2018 0‘Ruƙiyya’ asalin kalmar  daga Larabci ne ‘Ruƙyah’ amma Hausawa suka mayar da ita ‘Ruƙiyya’. Bisa ga haka, za a ci gaba da amfani da kalmar Ruƙiyya a wannan muƙala. Ruƙiyya wata hanya ce ta samun waraka daga rashin lafiya musamman wadda ta shafi cutar iskoki. Duk da kasancewar ruƙiyya ta samo asali tun daga Mazon Allah (SAW), amma a ƙasar Hausa da maƙwabtanta, sha’anin ruƙiyya ya zama kamar wani sabon abu. A goshin ƙarni na ashirin da ɗaya, farkon shigowar ruƙiyya an samu saɓani da zanga-zanga na halaccin ta, daga ɓangarorin malaman addinin Musulunci. Malaman Ƙungiyar Izala su suka karɓi ruƙiyya da aiwatar da ita bisa ga tsarin da ta zo...

Friday, December 28, 2018

Tasirin Fina-finai A Kan Al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi’u Na Musamman a Cikin Fina-finan Hausa

December 28, 2018 0


An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da saƙwanni ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin sun shafi ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka haɗa da Turawa, da Indiyawa da sauransu. Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da ƙwarƙwa kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da